Indiya: Zabtarewar kasa ta kashe mutane 14
June 30, 2022Talla
Ma'aikatan bayar da agajin gaggawa yayin afkuwar bala'o'i da 'yan sanda da mazauna kauyen na kokarin ceto wadanda ke binne a karkashin kasa, a wani gari kusa da Imphal babban birnin jihar Manipur.
Hukumomi sun bayyana cewa zabtarewar lakar ta lalata layukan dogo tare da haddasa barna mai yawa da zuwa yanzu ba a tantance adadinta ba.