1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaftarewar dusar kankara ta rufta da sojojin Pakistan

April 7, 2012

Dusar kankara a yankin tsaunukan Himalaya ta rufta da sojin Pakistan fiye da 100. Jami'an agaji na ci-gaba da aikin ceto amma babu tabbas game da wadanda suka tsira.

(FILES A file photograph showing a Pakistani Army helicopter flying in the outskirts of Skardu near Siachen where the world's biggest glaciers lies, Sunday 15 May 2005. The Indian Army has rejected a possible compromise with Pakistan over the disputed Siachen glacier, days before the peace talks between the South Asian neighbours are to begin, media reports said Sunday 12 November 2006. Senior Indian Army officers said Siachen was strategically important for India and that the military had no intentions of withdrawing troops as it occupied vantage positions on the glacier. EPA/OLIVIER MATTHYS +++(c) dpa - Report+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Sojojin Pakistan fiye da dari daya (100) ne zaftarewar dusar kankara ta binne a wani sansaninsu dake Gayari a yankin Himalaya wanda ke kan iyaka da kasar India a wannan Asabar. Lardin Siachen dake arewaci shine zirin da ya raba yankin Kashmir inda kasashen biyu na Indiya da Pakistan suka dade suna takaddama akansa kowa na cewa yankinsa ne. Wasu rahotanni sun ce yawan sojojin da dusar kankarar ta rufta da su sun kai 150. Kakakin rundunar sojin Manjo janar Athar Abbas yace an tura ma'aikatan ceto zuwa yankin a jiragen sama masu saukar ungulu domin kai dauki. Manjo janar Abbas ya ce ba'a sami wani labari ba game tabbacin ko akwai wadanda suka tsira da rayukansu. A cikin wata sanarwa Firaministan Pakistan Yousuf Raza Gilani ya baiyana kaduwa da aukuwar lamarin.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Saleh Umar Saleh