1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Zaftarewar kasa ta halaka mutane a kasar Kamaru

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
November 7, 2024

Ministan ayyuka na kasar Emmanuel Nganou Djoumessi ya ce ruwan sama mai karfi ne ya janyo zaftarewar kasar.

Motar bayar da agajin gaggawa a kasar Kamaru
Hoto: Joel Kouam/AP Photo/picture alliance

Hukumomin kasar Kamaru sun tabbatar da mutuwar mutane hudu, yayin da wasu 50 kuma suka yi batan dabo, bayan kifewar motoci 3 dauke da fasinjoji, sandiyyar zaftarewar kasa a yammacin kasar.

Yayin ziyara a wurin da lamarin ya faru, ministan ayyuka na kasar Emmanuel Nganou Djoumessi, ya ce ruwan sama mai karfi da aka samu a kasar ranar Talata shi ne ya janyo zaftarewar kasar, a kan babban hanyar da Dschang, da ke hadewa da Douala cibiyar kasuwancin Kamaru.

Karin bayani:Kamaru ta hana magana kan rashin lafiyar Paul Biya

Ministan ya umarci a mika gawarwakin mutane hudun da aka gano zuwa wajen ajiyarsu, kuma a bai wa wadanda suka samu raunuka kulawar gaggawa don ceto rayukansu, sannan kuma masu aikin agaji su ci gaba da laluben sauran mutane hamsin din da suka bace.