1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Zaftarewar kasa ta hallaka mutane 22 a Tanzania

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
January 14, 2024

Tanzania da sauran makwabtanta na gabashin Afirka, da suka hada da Kenya da Somalia da Ethiopia, na fama da ambaliyar ruwa sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da suka fuskanta, mai alaka da yanayin zafi na El Nino

Hoto: Tanzania’s Ministry of Interior

Shugabar Tanzania Samia Suluhu Hassan ta tabbatar da mutuwar mutane da 22 sakamakon zaftarewar kasa a mahakar ma'adanai ta Ng'alita da ke Bariadi a yankin Simiyu na lardin arewacin kasar.

Karin bayani:Sabon rukunin 'yan kasuwa a Tanzaniya

Shugaba Samia Suluhu Hassan ta wallafa hakan ne a Lahadin nan a shafinta na X da aka fi sani da Tiwita a da, ta na mai cewar wadanda suka mutu talakawa ne da ke aikin hakar ma'adanai domin samun abin da za su ciyar da iyalansu, har ma da bunkasa tattalin arzikin kasar.

Karin bayani:Yaki da nuna wariya da kyama ga Zabiya

Tanzania da sauran makwabtanta na gabashin Afirka, da suka hada da Kenya da Somalia da Ethiopia, na fama da ambaliyar ruwa sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da suka fuskanta, mai alaka da yanayin zafi na El Nino.