1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIndiya

Rayuka sun salwanta a zaftarewar kasa a Indiya

July 30, 2024

Wani sabon ibtila'in zaftarewar kasa da ya auku a Indiya, ya salwantar da rayukan sama da mutum 40 a wannan Talata, yayin kuma da ake fargabar wasu da dama kuma na karkashin kasa.

Hoto: CK Thanseer/REUTERS

Hukumomi na kudancin jihar Kerala da ke kasar Indiya su ne suka tabbatar da faruwar lamarin a yankin, bayan ruwan sama kamar da bakin masaki da aka yi ta shatatawa.

Sama da mutum 40 dai sun rasa rayukansu ciki har da wani jariri, yayin da wasu da dama ke makale a karkashin kasa.

Jami'an agaji sun bayyana takaicin rashin iya kai agaji cikin lokaci, saboda yankewar da wata muhimmiyar gada da ke gundumar Wayanad ta yi.

Rundunar sojan kasar ta Indiya dai, ta ce ta aike da dakaru 200 zuwa yankin domin taimaka wa jami'an da ke wajen wadanda ke kokari ta fannin dauki ga masu bukata.

Ko a shekara ta 2018 ma dai zaftarewar laka ta kashe akalla mutum 500 a kewayen yankin na Kerala, bala'in da aka bayyana da mafi muni cikin shekaru da dama.