1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zagayen karshe na zaben yan majalisun dokoki a Masar

December 7, 2005

A kasar Masar yau ne a ka shiga gangara karshe a zaben yan majalisun dokoki.

Saidai wannan zagaye, ya fuskanci tashe tashe hankulla, da kungiyar yan uwa musulmi ta dangata, da aikin da gangan, da gwamnati ta shirya, da nufin sa tarnaki, ga gagaramar nasara da yan takara da kungiyar ta jera, ke shirin samu.

A rufunan zabe da dama jami´an yan sanda sun yi anfani da barkonontsohuwa domin tarwatsa mutanen da suz ka zo zabe, kazalika sunci gaba da capke wanda su ka nuna taurin kai.

A jimilce, kujerun yan majalisa 120 ne ,za a zabe a yau.

Ya zuwa yanzu, daga jimmilar kujeru 454, da majalisar dokokin Masar ta kunsa, kungiyar yan uwa musulmi ta lashe kujeru 76. Saidai duk da wannan nasara, jamiyar PND ta shugaba Osni Mubarak ta samu rinjaye a Majalisa.

Kakakin gwamnatin Amurika ya bayyana damuwa, a game da tashe tashen hankulla da ke tattare, da zabukkan na Masar, ya kuma yi kira ga gwamnati, da ta dauki mattakan da su ka dace, domin tabatar da adalci.