1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Zagayen majalisar mashawarta ta Jamhuiryar Nijar

Salissou Boukari SB
February 26, 2026

A Jamhuriyar Nijar mambonin Majalisar mashawarta ta kasa sun soma wani rangadi a jihohi takwas na kasar inda za su tattauna da jama'a don sanar da su mahimman batutuwa da suka shafi tsaron kasa.

Majalisar mashawarta ta Jamhuriyar Nijar
Majalisar mashawarta ta Jamhuriyar NijarHoto: Salissou Boukari/DW

A Jamhuriyar Nijar, a wani mataki na zaburar da al'ummar kasa kan fannoni da dama musamman na tsaro da kishin kasa, Mambonin Majalisar mashawarta ta kasa sun soma wani rangadi a jihohi takwas na kasar.

Inda za su tattauna da jama'a don sanar da su mahimman batutuwa da suka shafi tsaron kasa ta yadda kowa zai rungumi matsalar kasa a matsayin tashi ce ba ta wani ba, don ganin kowa ya ba da hadin kai wajen kariyar kasa da ci-gabanta. Sai dai kuma har yanzu majalisar na ci gaba da fuskantar suka daga yan kasar da dama.

Dalilan rangadin

Majalisar mashawarta ta Jamhuriyar NijarHoto: Salissou Boukari/DW

Kafin dai take soma wannan aiki na ziyartar jihohin kasar inda suke gudanar da ayyuka na fadakarwa tare da hukumomin yankin da suke, Majalisar mashawarta ta kasar ta Nijar ta sha suka dagako'ina ta kafofin yada labarai da na sadarwa kan batun kasafin kudi na Majalisar.

Sai dai kuma anaganin wannan wata dama ce ga jagororin majalisar na su taka rawar gani wajen fadakar da al'umma kan batun nan mai tarin mahimmani na tsaro da shi kanshi aikin majalisar.

Sanin kowane dai a baya kasar ta Jamhuriyar Nijar ta fuskanci tarin matsaloli na game da kashin kudi a iri-irin wannan manyan ma'aikatu kaman majalisar dokoki da ‘yan kasar da dama suke mata kallon jeka na yi.

Sannan a baya wasu sun yi ta amfani da matsayinsu wajen wawushe kudadan kasa, wanda a yanzu kuma da kasar ta rungumi sabon tsari na sabuwar tafiya, wasu ke ganin ya kamata a samu sauyi. Sai dai ga wannan karo a cewar ‘yan majalisar mashawartan akwai bambamci sosai.

Abin da masana ke gani

Majalisar mashawarta ta Jamhuriyar NijarHoto: AFP

Ga masu sharhi kan dokokin shari'a irin su Docta Atto Namaiwa, Malami a jami'ar birnin Tahoua, wanda tun tashin farko ya nuna rashin gamsuwarsa da tsarin kafa wannan majalisa ta masharwa da ya ce ba ta da wani karfin iko, har yanzu yana kan bakansa na ganin cewa majalisar ba ta cancanci gudanar da wannan rangadi ba, ta la'akkari da gamnati na da wakillai a ko'ina a fadin kasa.

Su dai mambobin majalisar mashawarta duk da cewa ba zabe aka yi irin na dimukuradiyya aka dauke su ba, amma kuma akasarinsu mutane ne da ke da gada a ji a yankuda suka fito, wanda ake ganin idan sun fuskanci jama'a a irin wannan aiki na fadakarwa, za ta iya sauraronsu da kunnuwan basira, ko ma da yake wasu na ganin cewa da kamata ya yi kowane mashawarci ya yi wannan aiki a matsayin na sa kai a yankin da  ya fito, maimakon tayar da tawagogi zuwa yin wanan rangadi.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani