1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaki ya kashe mai ba shi abinci a Iran

Abdul-raheem Hassan
January 30, 2022

Wani zaki ya kashe mai kula da shi a kasar Iran yayin da yake ciyar da shi abincin rana, sannan ya tsere da matarsa a wani gidan namun daji kafin a kama su.

Zaki
Hoto: Pippa Henkinson/Blood Lions /AP/picture alliance

Kamfanin dillancin labaran IRNA da ke kasar Iran, ya bayyana cewa marigayin mai suna Esfandani yana da shekaru 40, kuma ya gamu da ajalinsa ne bayan da Zakin ya kubuce daga keji lokacin da ya ke sa mishi nama ta taga, sannan ya gudu da matarsa.

'Yan sanda da masu gadi sun kama zakunan biyu bayan 'yan sa'o'i suna neman hanyar fita daga gidan dabbobin wanda yake a tsakiyar birnin Arak, kimanin kilomita 200 Kudu maso yammacin Tehran babban birnin kasar Iran.

Hukumomi na gudanar da bincike kan kashe mutumin da Zakin ya yi, ko da yake ana yawaita samun kubucewar namun jeji daga gidajen adana dabbobi a kasar Irin, kuma galibi ana zargin rashin matakan tsaro a wasu gidajen adana namun jejin na haifar da barazana.