Jayayya tsakanin Habasha da Eritrea kan tashar jiragen ruwa
November 15, 2023
A lokacin da firirmiyan Habasha Abiy Ahmed ya hau kan mulki a shekara ta 2018, ya kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakaninsu da makobciyarsa Eritrea, abin da ya kawo karshen gaba mai tsawo tsakaninsu. Wannan dai shi ne ya kai ga bai wa Abiy Ahmed damar samun kyautar zaman lafiya ta Nobel. S daia ya nzu ana cike da tsoron ka da dukkan kokarin da aka yi shekaru biyar da suka gabata ya wargaje. Abdurehman Seid masharhancin siyasa ne kan yankin kahon Afirka da Gabas ta Tsakiya.
Habasha ta yi watsi da Amhara da Eritrea wadanda wadanada suka taimaka wa gwamnatin Habasha yakar TPLF.
'' Shugaban kasar Eritrea Isaias Afeworki na ganin cewa yakin basasa da aka yi tsakanin Habasha da mayakan Tigray bai tsinanan sakamakon da ake bukata ba. Domin yakin bai kai ga murkushe mayakan Tigray na TPLF ba. Bugu da kari shi ne yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Habasha da mahukuntan Tigray na nufin TPLF za su ci gaba da iko da dukkannin yakunan da ke a hannunsu. Bisa hakan firaministan Habasha a takaice ya wayi watsi da Amhara hade da Eritrea, wadanda duk suka taimaka wa gwamnatin Habasha yakar TPLF.”
Yaki na shirin barkewa tsakanin Habasha da Eritrea
Tashar jiragen ruwa da ake magana ta Assab, na cikin kasar Eritrea wacce a da ke karkashin Hasbahja gabanin kasashen su rabu biyu kimanin shekaru 30 da suka gabata. Wanda kuma a cewar masanin siyasar yankin firaministan na Habasha da ya tado da batun tashar jiragen ruwa tamkar tada wani kurji ne. Shi firaminista Abiy Ahmed da ya tado da batun tashar jiragen ruwa a wannan lokacin ya yi haka ne kawai don kawar da hankulan jama'a kan rushewar tattalin arziki da rikicin sojojnin da yake fama da shi a cikin gida. A nan bangaren ina jin zai taimaka masa a siyasance, amma ga shi firaminista Abiy bana jin zai kuskura ya ce zai mamaye Eritrea, kai ko da ma yana son yin hakan, ba na ganin yana da karfin aiwatarwa”
A lokacin da Eritrea ta ayyana samun yancin kai, ta yi ta buga kirjin mallakar tashar jiragen
Tun shekarar 1998 Habsha ta rasa damar amfani da tashar biyo yakin sama da shekaru 20 tsakanin kasashen biyu, wanda duk wani kayan da ya shafi tashar jiragen ruwa dole sai ta makobciyarsu Djibouti ake shigo da su. Yesuf Yasin tsohon jami'in diflomasiyya ne kana masanin siyasar yakin. ''A lokacin da Eritrea ta ayyana samun yancin kai, ta yi ta buga kirjin mallakar tashar jiragen ruwan, sun yi ta bayyana habaka tashar, kai wasu masharhanta ma sun yi ta bayyanan mahimmanci da tashar ke da shi. To amma yanzu bisa takaddama da rashin zaman lafiya, walau Eritrea ko Habasha ko ma al'ummar da ke rayuwa kusa da tashar jiragen ruwan babu wanda ke amfana da ita”
Habasha na buktar tashar jiragen ruwa ta Assab ta kowane hali
Firaministan Habasha Abiy Ahmed, an jiyo shi yana mai cewa kasar na bukatar tashar jiragen ruwa, kuma ba wai sai ta sha wahala ta samu hakan ba. Inda ya yi hannunka mai sanda kan shirin kasarsa na samu damar amfani da tashar jiragen ruwan Assab wace ke cikin Eritrea. Kai tun watan juni lokacin taro da 'yan kasuwa firaministan Habasha ya fada masu cewa kasara na bukatar samun tashar jiragen mallakarta cikin ruwan sanyi, amma kuma in ta kama ko da karfi za su yi hakan. Wadannan kalaman nasa dai sun kara kawo zaman dar-dar a yankin da dama ya yi gwammam shekaru bai ga zaman lafiya ba.Tashin hankali na karuwa a yankin Amhara