1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman jiran sakamakon zaben Kenya

March 7, 2013

An yi suka ga aikin kidayar kuri'u dake tafiyar hawainiya, inda dukkan bangarorin da abin ya shafa ke saka ayar tambaya ga sakamakon da za a bayar.

Kenyan Independent Electoral and Boundaries Commission (IEBC) officials finalise ballot-counting at a polling station on March 6, 2013 in the Mathare slum, in Nairobi. Kenyans awaited presidential results with growing frustration at controversial delays and mountains of spoiled ballots, five years after violence sparked by a disputed tallying process. AFP PHOTO / SIMON MAINA (Photo credit should read SIMON MAINA/AFP/Getty Images)
Hoto: SIMON MAINA/AFP/Getty Images

Kawancen 'yan siyasar Kenya karkashin jagorancin Piraministan Raila Odinga, a wannan Alhamis sun ce aikin kidayar kuri'un da ake yi yanzu don tantance mutumin da yayi nasara a zaben shugaban kasar, bai da inganci kuma ya kamata a dakatar da shi. Kawancen yayi zargin cewa an yi sauya wasu daga cikin sakamakon zaben da aka samu kawo yanzu.

Sanarwar da kawancen 'yan siyasar wato CORD karkashin jagorancin Raila Odinga daya daga cikin manyan 'yan takara biyu a zaben shugaban kasar ta Kenya ya bayar, ta ce ya kamata a sake kidayar kuri'un ta amfani da bayanan da aka tattara daga tashoshin zabe.

Sai dai shugaban hukumar zaben kasar Ahmed Issack Hassan ya fada wa wani taron manema labarai a Nairobi cewa babu yadda za a iya taba sakamakon zaben kuma za a sanar da sakamakon karshe cikin daren wannan Alhamis ko kuma ranar Juma'a.

"Hukumar zabe na tabbatar wa al'umar Kenya cewa dangane da tsauraran matakan da aka dauka, babu yadda za a yi a canza sakamakon zaben. Duk wani bature zabe da yayi yunkurin sauya sakamakon ko boye kuri'ar da aka kada, to za fuskanci hukunci mai tsanani kamar yadda doka ta tanada."

Ya zuwa wannan yammacin mukaddashin Piraminsita Uhuru Kenyatta ke kan gaban Raila Odinga da yawan kuri'u ko da yake yawan kuri'un da aka tattara yanzu ba su kai na rabin tashoshin zabe ba.

Uhuru KenyattaHoto: Getty Images

Fargabar sake aukuwar rikicin bayan zabe

A ranar Litinin da ta gabata kasa ta Kenya ta gudanar da zaben kasa baki daya karon farko tun bayan zaben shekarar 2007 da ya janyo rigingimun kablanci da ya halaka mutane sama da dubu daya. An samu bore jama'a nan da can tun bayan zaben na ranar Litinin sai dai babu wani mummunan rikicin kabilanci shigen na shekarar ta 2007. Amma yayin da lokaci ke tafiya ba tare da samun cikakken sakamako ba, hankali na tashi, abin da ke sanya fargabar cewa wani rikici ka iya barkewa, musamman ma zargin da ake game da yin aringizon kuri'u.

Parfesa Anyang Nyong na kawancen 'yan siyasar ya soki lamirin hukumar zaben in da ya ce:

"A matsayinmu na shugabannin jam'iyun siyasa alhaki ya rataya wuyanmu mu ga cewa sakamakon da aka bayar daga mazabu ya dace da gaskiyar abin da jama'a ta zaba. Idan jami'an zabe sun sauya wannan sakamako, hakan ya saba da doka da ka'idojin zabe."

Rashin yarda ya yi yawa

Daga bangaren Uhuru Kenyatta ma dai an soki lamirin hukumar zaben, kamar yadda wani mai goyon bayansa ke cewa ne da wuya wata jam'iya ta amince da sakamakon zaben.

Raila OdingaHoto: Reuters

"Idan Raila Odinga ya yi nasara, za mu garzaya kotu. Mun sa kuma cewa idan shugabanmu Uhuru Kenyatta ya ci su ma kawance CORD za su je kotu. Dukkan wadannan abubuwan ba su dace ba. Ba sauran abin da za ka yarda shi yanzu."

Tun a ranar Laraba hukumar zaben kasar ta amsa cewa sabuwar fasahar da ta kirkiro kanta ta aikewa da sakamakon daga mazabu, ba ta aiki. Saboda haka shugaban hukmar Issack Hassan ya yi kira ga dukkan shugabannin mazabun da su gaggauta kai takardun sakamakon daga ofishoshin zabe zuwa birnin Nairobi.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe