Zaman lafiya a gabas ta tsakiya.
August 16, 2006Talla
Shugaban ƙasar Syria Bashar al-Assad yace akwai shakku a game da samun zaman lafiya mai dorewa a gabas ta tsakiya matuƙar shugaban Amurka George W Bush na kan karagar mulki. Yace aƙidar Bush na yaƙin babu gaira babu dalili ya sabawa buƙatar wanzar da zaman lafiya. Bashar al-Assad ya kuma jinjinawa Hizbullah bisa abin da ya baiyana da cewa gagarumar nasara da suka samu a kan Israila a kudancin Lebanon. Yana mai cewa Syria na alfahari da nuna goyon baya ga dakarun Hizbullah. A waje guda kuma ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmier ya baiyana kalaman shugaban ƙasar Syria Bashar al-Assad da cewa bai dace ba. Steinmier wanda ya shirya kai ziyara ƙasar Syria ya soke ziyarar tasa.