1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tabbatar da zaman lafiya a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

Suleiman Babayo LMJ
November 5, 2024

Kasashe uku sun kaddamar da kwamtin saka idon kan yarjejeniyar zaman lafiya a a yankin gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.

Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango | Sojoji suna aiki a garin Goma
Sojojin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango suna aiki a garin GomaHoto: Wang Guansen/Xinhua/picture alliance

Ministocin harkokin wajen kasashen Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Ruwanda sun jaddada muhimmancin ci gaba da girmamama yarjejejiyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin da ke riki a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. Ministocin sun gana tare da ministan harkokin wajen Angola a birnin Goma fadar lardin arewacin Kivu na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, inda aka kaddamar da kwamiti tsakanin kasashen Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Ruwanda domin kula da shirin samar da zaman lafiya a yankin.

Karin Baynai: Gabashin Jamhuriyar Demokaradiyya Kwango cikin halin yaki

An kulla yarjejenyiar tsakanin dakarun Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da 'yan tawayen kungiyar M23 mai samun goyon bayan Ruwanda. Shi dai Tete Antonio ministan harkokin wajen kasar Angola ya tabbatar da wannan bayanan bayan ganawa tsakanin manyan jami'an diflomasiyyan kasashen.

Ita dai Therese Kayikwamba Wagner ministar harkokin wajen kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ba ta ce komai ba bayan wannan ganawa.