Burkina Faso: 'Yan ta'adda sun kashe mutum 79
June 14, 2022Talla
A daren Asabar zuwa Lahadi wasu mutane dauke da makamai suka kashe fararen hulan a wani hari da suka kai a kauyen Seytenga dake a rewacin Burkina Fason kan iyaka da Nijar. Koi'na a cikin ofisoshi gwamatin na cikin gida da ketare an yi kasa-kasa da tuttocin kasar domin girmama wadanda suka mutu.Wanda ke daya daga cikin hare-hare mafi muni da aka kai, tun bayan da sojoji suka karbi mulki a cikin watan Janairun da ya gabata.