Zaman sulhu kan rikicin gabashin Ukraine
December 24, 2014![Terffen zwischen Poroschenko und Lukaschenko in Kiew](https://static.dw.com/image/18145042_800.webp)
Talla
Tattaunawa tsakanin bangarorin dai a 'yan makonnin da suka gabata ta sha fama da cikas, to sai dai a wannan karon masu shiga tsakani a tattaunawar wadda za ta wakana a birnin Minsk na kasar Belarus na son ganin an samu cigaba mai ma'ana.
Zaman na yau dai na zuwa ne bayan da Rasha ke cigaba da yin jan ido dangane da aniyar da Kiev ta dauka na shiga kungiyar tsaro ta NATO, shirin da shugaban Ukraine din ya ce ba gudu ba ja da baya.