Zaman sulhu kan rikicin Libiya
January 10, 2015Talla
Manzon musamman ma Majalisar ta Dinkin Duniya Bernardino Leon ya ce tattaunawar na da muhimmancin gaske duba da yadda kasar yanzu ke cikin wani yanayi na rashin tabbas.
Tattaunawar inji Mr. Leon za ta maida hankali ne wajen samar da wani yanayi da zai kawo karshen rikicin da bangarorin ke yi a kasar da samar da gwamnatin hadin kan kasa gami da kaiwa ga samar da sabon kundin tsarin mulki.
Kasashen duniya dai na cigaba da nuna fargabarsu ta dagulewar lamura baki daya a Libya din muddin ba a dauki mataki kan rikicin kasar cikin gaggawa ba.