1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta gargadi kungiyar Hezbollah

Suleiman Babayo ZMA
July 28, 2020

Shugbaannin Isra'ila sun yi gargadin sojojin musamman na kasar suna shirya da kutsawa Lebanon muddun kungiyar Hezbollah ta kaddamar da sabbin hare-hare cikin Isra'ila.

Israel Libanon | Konflikte an der Nordgrenze
Hoto: AFP/J. Marey

Firaminista Hassan Diab na kasar Lebanon ya zargi gwamnatin Isra'ila da keta iyakar kasar amma ya bukaci yin taka tsantsan sakamakon zaman tankiya da ake samu kan iyakar kasashen. Firaministan ya fadi haka lakacin taron koli na tsaron kasar.

Wannan na zuwa lokacin da Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila da ministan tsaronsa Benny Gantz suka fitar da sanarwar hadin gwiwa ceto sojojin musamman na kasar suna shirya da kutsawa Lebanon muddun kungiyar Hezbollah ta kaddamar da sabbin hare-hare cikin Isra'ila daga kasar ta Lebanon. Gwamnatin Isra'ila ta yi gargadin bayan makamun roka da ta harba ya halaka wani babban jami'in kungiyar ta Hezbollah. Gwamnatin Lebanon ta dauki harin akan abin da ya saba kudirori da dokoki na kasashen duniya.