Zaman warwarerikicin nuclear koriya ta arewa
December 16, 2006Talla
Jakadan kasar Koria ta arewa a tattaunawar rikicin nuclearn kasar a Beijing ya bayyana cewa,kasarsa bazata yi watsi da shirin nuclearnta ba ,har sai Amurka ta dakatar da miyagun manufofinta da dakatar da takunkumin tallafi,data kakabawa Pyangyong.Mataimakin ministan harkokin waje na Koriyan Kim Kye-Gwan,yace har yanzu da sauran lokaci ,adangane da da cimma wani tudun dafawa a wannan sabon zagayen tattaunawa da aka koma a ranar jumaa a Beijin ,tsakanin Koriyoyin biyu da Sin da Amurkan da Rasha da Japan.Mr Kim ya fadawa manema labaru cewa abu mafi muhimmanci shine wa Amurka ta sauya manufofinta akan kasar Koriya ta arewan.