1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaZambiya

Zambia ta dakatar da sanar da sakamakon zabe

August 14, 2026

Hukumar zabe ta kasar Zambia ta dakatar da sanar da sakamakon babban zaben kasar, sakamakon hare-haren da aka kai wa jami'an zabe.

Shugaban Zambia Hakainde Hichilema
Shugaban Zambia Hakainde HichilemaHoto: Ben Curtis/AP Photo/picture alliance

Hukumar ta ce ta samu rahotannin sace takardun kada kuri'a a wasu wurare, a don haka za ta sake nazarin matakin dakatarwar cikin sa'o'i 24.

Kimanin mutane miliyan takwas ne suka yi rajistar kada kuri'a a Zambia, mai yawan al'umma kusan miliyan 22. Baya ga zaben shugaban kasa, ana kuma zaben 'yan majalisar dokoki da kansiloli a rumfunan zabe sama da 13,500.

Karin bayani : Yan Zambia sun yi zaben shugaban kasa

Masu sa ido sun ce an samu dogayen layuka da tsaiko a wasu rumfunan zabe, da kuma rudani kan jerin sunayen masu kada kuri'a.

Zaben na zama babban gwaji ga shugaba Hakainde Hichilema, wanda ke fuskantar dan takarar adawa Brian Mundubile, jagoran kawancen 'yan adawa da ke samun goyon bayan tsohon shugaban kasar Edgar Lungu.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW