Soma zaman shari'ar Kambwili a Lusaka
June 18, 2018A kasar Zambiya wata kotun birnin Luzaka ta fara a wannan Litinin zaman shari'ar Chishimba Kambwili dan siyasar nan da ya yi kaurin suna wajen caccakar shugaban kasar Edgar Lungu. A watan Maris din da ya gabata ne dai aka kama Mista Kambwili a gidansa da ke a birnin Lusaka a bisa zargin aikata wasu laifuka har 39 da suka hada da na mallakar wasu gidaje ta hanyar amfani da wasu kudaden da ya samo ta haramtacciyar hanya.
Sai dai kuma da yake kare kansa a wannan Litinin a gaban kuliya dan siyasar mai shekaru 48 wanda kuma dan majalisa ne daga jam'iyya mai mulki ta Front Patriotique ya yi watsi da illahirin zarge-zargen da ake yi masa yana mai cewa a shirye yake ya kawo hujjoji na halittattun hanyoyin da ya bi wajen samun wadannan kudade nasa.