Ruwa ya ci mutane a Zamfara
October 6, 2022Talla
Rahotanni daga jihar Zamfara da ke Arewa Maso Yammacin Najeriya na nuni da cewa mutane da dama ne sun rasa rayukansu a garin Birnin Waje da ke karamar hukumar Bukuyum sakamakon nutsewa a ruwa a lokacin da suke kokarin gudun tsiratar da rayukansu. Wani shaidan gani da ido ya bayyana DW cewa, mutanen sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da wasu 'yan bindiga suka farwa al'ummar garin. Kakakin rundunar Yan sandan jihar ta Zamfara SP Shehu Muhammad ya tabbatar da afkuwar lamarin sai dai ya ce ba 'yan bindiga bane suka biyo wadanda suka rasa rayukansu.