1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Soke hukuncin kotu kan zaben fidda gwani na APC a Zamfara

March 25, 2019

Wata kotun daukaka kara ta gwamnatin tarayya da ke Sakkwato ta rushe hukuncin kotun jihar Zamfara da ta bayar cewa jam'iyyar APC a jihar ta yi zabukan fidda gwani.

Nigeria Oppositionspartei APC
Hoto: DW/K. Gänsler

Zabukan fidda gwani ne dai suka samar da 'yan takarar majalisun tarayya da na jiha da kuma na gwamna wanda tuni jam'iyyar APC a jihar Zamfara ta lashe baki daya a babban zaben da a gudanar. Sai ga kuma wannan hukuncin kotu na soke halarta zabukan fidda gwanin wanda mai Shari'a Tom Yakubu ya jagoranta. Hakan za a iya cewa ya maida wa jam'iyyar APC a jihar Zamfara hannun agogo baya. Wannan hukunci ya faru ne sakamakon daukaka kara da masu adawa da gwamnatin jihar Zamfara suka yi da ake kira G8 suna kalubalantar zabukan fidda gwanin, inda suke zargin an yi dauki dora.

Barrister Musbahu Salahudden shi ne lauyan masu shigar da kara ya yi wa manema labaru karin bayani jim ka dan bayan fitowa daga zaman kotun.

"Gaskiya ta bayyana yau a gaban kotu in da manyan alkalai suka rushe hukuncin Honarabul Justice Bello Shinkafi na Gusau. Sun ce ba a yi zaben fidda gwani ba, sun ce amfanin doka shi ne binta."

Masu kalublanar zaben sun ce dauki dora aka yi amma ba zabe baHoto: DW/K. Gänsler

Brister Surajo Garba Gusau na daya daga cikin tawagar lauyoyin jam'iyyar APC a wurin shari'ar shi ma ya yi karin haske yana mai cewa.

"Bayan an shiga kotu ne su alkalan suka karanta hukunci abin da suka ce shi ne akwai takaddama da hukumar zabe ta aika wa Adams Oshiomhole take cewa ba a yi zabukan fidda gwani ba. Sannan akwai kuma takarda da shi shugaban jam'iyyar APC na jihar Zamfara shi ma ya aika sannan akwai takardar da shi Adams Oshiomhole ya sake aika ma INEC cewa ai za su sa 'yan takara a jihar Zamfara. To wadannan abubuwan ne suka duba sannan suka ce akwai shaida ya taho ya ba da shaidar ta baki, ya ce akwai kwamitoci guda biyu sun ba da shaida. To amma abin da suka ce shaidar baki ba ta rinjayar shaidar takarda. Don haka sun fi ba waccen takardar karfi, don haka suka ce abin da kotu ta yi ta aminta da cewa lallai waccen kotun abin da ta yi ba ta yi bincike sosai ba."

To ko yaya masana shari'a ke kallon wannan hukunci? Justice Sadiq Abdullahi Mahuta tsohon babban jojin jihar Katsina ne, ya yi karin bayani.

"Ga alama wannan kotun daukaka kara ta Sakkwato ta ce daya daga cikin ka'idojin da aka gindaya ba a yi amfani da su ba, don haka kamar ka gina gida ne bisa yashi, ai kasan ba magana rushewa zai yi. Wannan hukunci ya rushe wannan zabe saboda haka sai a saurara a ga kotu idan za ta aika da takardarta zuwa INEC. Sai dai jam'iyyar APC na da damar daukaka kara nan gaba zuwa kotun koli."

Jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara ta shigar da kara gaban babbar kotun jihar a kan zabukan fidda gwanin, inda babbar kotun ta halarta mata cewa an yi zabukan fidda gwanin su kuma bangaren masu adawa da gwamnati da ake kira G8 suka kalubalanci wannan mataki har zuwa wannan babbar kotun daukaka kara, wanda hakan ne ya ba su nasarar soke hukuncin kotun ta Gusau.