Zamfara ta karbi tuban Bello Turji
August 23, 2022Talla
Wannan bayani na kunshe ne a jawabin da mataimakin gwamnan jihar Zamfara ya yi inda ya tabbatar da cewa gwamnati ta karbi tuban dan bindigar.
Mataimakin gwamnan jihar ta Zamfara Hassan Nasiha ya ce tun bayan da suka cimma matsaya game da tuban dan bindigar, yanzu fiye da makwanni shida ke nan ba a sami asarar rai ba da ya danganci ayyukan 'yan ta'adda a jihar.
A watan Yunin da ya gabata ne gwamnan jihar ta Zamfara Bello Mohammed Matawalle ya umurci mataimakinsa da ya jagoranci tattaunawar sulhu da 'yan bindigar, yanzu haka Turji na sanar da bukatar a sako masa 'yan bindigar da ke hannun gwamnati da kuma kawo karshen kisan da ya ce ana yi wa fulani 'yan uwansa.