1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zamfara ta sake dawo da layukan sadarwa

November 29, 2021

Gwamnatin jihar Zamfara a Najeriya ta sanar da dawowa da layukan sadarwa da aka katse na tsawon watannin uku da nufin kawo karshen matsalar tsaro da jihar ke fuskanta.

Karte - Nigeria, Bundesstaat Zamfara - DE

Tun dai a ranar Asabar din data gabata ne dai gwamnan jihar Bello Matawalle ya ce an sami gamsassun rahotannin da ke nuna cigaban da aka samu bayan daukar tsauraran matakan, wanda ya katse duk wata hanyar sadarwar tsakanin 'yan bindigar da ke jihar da kuma jihohin Kaduna da Katsina da kuma Niger. A watan Satumbar data gabata ce dai kamfanonin sadarwar a jihar suka katse layukan waya, lamarin da ya haifar wa mazauna jihar da dama zuwa makwaftan garuruwa da nufin kiran waya da kuma sauran harkokin da suka shafi na bankuna.

A ranar Juma'ar data gabata ce dai ita ma jihar Kaduna ta sanar da dawo da layukan sadarwa da aka katse a wasu sassanta. Yankunan tsakiya da kuma arewa maso yammacin Najeriya na fuskantar hare-haren 'yan bindiga, wadanda ke satar shanu da yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa.
 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW