1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An tsawaita wa'adin toshe kafofin sadarwa a Zamfara

September 17, 2021

Gwamnatin jihar Zamfara da ake Arewa maso yammaci Najeriya ta ce ba za a janye dokar katse layukan waya a jihar ba har sai baba ta gani, a wani mataki na kara tunkarar matsalolin tsaro da suka addabi arewacin kasar.

Symbolbild I Hate Speech Spanisch
Hoto: Gerard Julien/AFP/Getty Images

Makonni biyun da suka gabata ne dai hukumar sadarwa ta Najeriya ta aiyyana rufe layukan wayar salula a jihar ta Zamfara na tsawon makonni biyu.

To sai dai a yayin da wa'adin rufe wayar salula ya kare a Zamfara a wannan Jumma'a, gwamnatin jihar ta ce ta kara wa'adin har ya zuwa samar da cikakken zama na lafiya mai tasiri a jihar.

Gwamnan Jihar ta Zamfara dai ya ce toshe kafofin sadarwar ya yi tasirin gaske a kokari na mayar da zama na lafiya cikin jihar.

Kuma a fadar Bello Matawalle da ke zaman gwamna na jihar, mahukuntan na Zamfara sun yanke hukuncin ci gaba a cikin karatun toshe wayar har illa ma Sha'Allah.

Makarantu a jihar Zamfara na daga cikin wuraren da 'yan bindiga ke far musu suna garkuwa da dalibaiHoto: Kola Sulaimon/AFP

Koma wane tasiri toshe wayar ke iya yi ga kokari na kaiwa ga zama na lafiya a Zamfara da ma a makwabtan jihohi dai, rufe sadarwa na kuma illa ga batu na tatttalin arzikin al'umma a jihar.

Ko bayan rushewa na kanana na sana'u a jihar, toshe wayar ta kuma toshe kafofin hada-hadar kudi da ke da tasiri a kasuwa cikin jihar da ma a makwabtanta.

To sai dai kuma a fadar Yahuza Getso da ke sharhi cikin batun rashin tsaron, "ba a bari a kwashe dai-dai cikin rikicin na Zamfara da ya bazu zuwa ga mafi yawa na jihohin yankin Arewa maso yammacin Najeriya."

Kokarin yi don Allah ko kuma siyasa da batun nan tsaro dai, tasirin toshe wayar a Zamfara ya sa akwai bukatar toshe waya a daukacin jihohin arewacin kasar a fadar gwamnan na Zamfara Bello Matawalle.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani