Hari kan Makiyaya a jihar zamfara
July 1, 2018
Talla
Wani wanda abun ya faru agaban idanunsa kuma aka kashewa 'yan uwa ya shaidawa wakilinmu Yusuf Ibrahim Jargaba cewa 'yan sa kan sun tare makiyayan ne lokacin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga jihar Naija, inda suka bude musu wuta.
Sai dai wani jami'an tsaro na sa kan a yankin da bai so a bayyana sunansa ba, ya shaidawa wakilinmu Yusuf Ibrahim Jargaba cewa basu da hannu wajen kisan Makiyayan. Rundunar 'yan sandan jihar ta Zamfara ta bakin kakakinta SP Shehu Muhammad ta tabbatar da afkuwar lamarin. Ko a ranar Juma'ar da ta gbata ma dai sai da wasu mahara suka hallaka mutane 11 a karamar hukumar Zurmi da ke jihar ta Zamfara.