Zamfara: 'Yan bindiga sun kashe mutane da dama
January 9, 2022
Talla
Wata mai magana da yawun ministar taimakon jinkai Sadiya Umar Faruk ta baiyana takaici da hare haren wadanda ke tagaiyara rayuwar al'umma da tilasta musu barin muhallansu.
Wasu mazauna kauyukan Anka da Bukkuyum sun ce 'yan bindiga sun hallaka mutane akalla fiye da 140.
Sai dai gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya ce mutane 58 ne aka kashe. Ya ce sarkin Anka ya bada sunayen mutane 22 da aka kashe yayin da Sarkin Bukkuyum ya bada sunayen mutane 36 da suka rasa rayukansu a hare haren.
A wannan makon gwamnatin Najeriya ta ayyana 'yan bindigar a matsayin 'yan ta'adda ta kuma ci alwashin daukar mataki domin murkushe su.