1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga zanga a ƙasar Aljeriya

January 8, 2011

Shugaban Aljeriya ya kiri taron majalisar ministoci bayan mutuwar mutane biyu a cikin zanga-zangar tsadar rayuwa a sassa daban-daban na ƙasar

Hoto: AP

Rahotanin daga ƙasar Aljeriya na cewa an samu asara rayuka a cikin zanga zangar da kungiyoyin ƙwadago da na fara hula ke gudanarwa a ƙasar sakamakon tsananin tsadar rayuwa da ake fama da shi. Rahotanin sun ce wani mutuman ɗan kimanin shekaru 32 da haihuwa ya rasa ransa a wani ƙawyen da ke da nisan kilomita 50 daga Aljes babban birnin ƙasar.

bMutumen mai sunan Alkriche Abdelfattah ya mutu bayan da ya shaƙi hayaƙi mai sa ƙwalla da jami'an tsaron suka jefa masa a fuska.Yayin da kuma wani matsashin, yan sandar su ka bindige shi har lahira a garin Misila da ke a yanki kudu maso gabacin Aljes

Gwamnatin ƙasar ta Aljeriya ta kira wani taron majalisar ministoci domin yin nazari akan hauhawar farashin kayan abinci da ya addabi al'umar.Foudi Bamala wani marubucin kanan kuma jami'in ƙungiyar kare hakkin bil adama ya ce gwamnatin ta yi jinkiri.Wannan taro da za su yi abun taƙaici ne domin kwanaki da dama ake ta yin tashin hankali a ƙasar akan halin da jama'ar suke ciki amma gwamnatin ta yi shuru sai yanzu bayan an riga an kashe mutane zasu ce su yi wani yunƙurin

Mawallafi :Abdourahamane Hassane

Edita : Yahouza Sadissou Madobi