Zanga zanga a ƙasar Taiwan
June 26, 2010Talla
Dubai jama'a sun gudanar da zanga zanga a birnin Taipei na ƙasar Taiwan, domin yin Allah wadai akan shirin saka hannu da gwamnatin ƙasar ta ke shirin yi akan wata yarjejeniya cinikaya tsakaninta da ƙasar China.
Masu zanga zangar wanda yawansu ya kai dubu ɗari sun riƙa rera kallamun na yin suka ga hulɗar ta kasuwanci da aka shirya ƙasashen biyu zasu rataɓa hannu a rana talata mai zuwa, wacce kuma suke gani wani mataki na kai ga cimma nassara hadewar ƙasashen biyu
ƙasahen Taiwan da China dai sun kasance da gwamnatoci biyu daban daban tun a shekara ta 1949 bayan yaƙin bassasar da suka yi ,to amma haryanzu ƙasar China na ɗaukar Tsibirin na Taiwan da cewa wani yankinta ne .
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita :Zainab Mohammed Abubakar