Zanga - zanga a Burkina Faso
February 7, 2015Dubban mutane ne suka fantsama kan tituna a Ouagadougu babban birnin ƙasar Burkina Faso domin buƙatar a rusa wata runduna ta musamman da ke bai wa shugaban ƙasa tsaro wadda ake tsoronta kwarai da gaske a ƙasar. Rundunar wadda aka fi sani da RSP na shan kakkausar suka saboda rawar da ta taka lokacin zanga-zangar da ya kai ga saukar tsohon shugaba Blaise Compaore daga mulkin da ya shafe shekaru 27 yana yi.
Aƙalla mutane 24 suka hallaka wasu 600 kuma suka yi rauni a wancan lokacin. Zanga-zangar ta ran Asabar wadda Ƙungiyoyin farar hula suka kira an yi shi ne a dandalin Revolution, dandalin da aka rika taruwa ana nuna adawa da Compaore.
Tun bayan saukar Compaore ƙasar na cigaba da kasancewa a hannun gwamnatin riƙo a ƙarkashin jagorancin Michael Kafando a matsayin shugaban ƙasa da Isaac Zida a matsayin Firaminista.