Zanga-zanga a Ireland.
November 27, 2010Talla
Ƙungiyoyin ƙwadago a ƙasar Ireland na gudanar da zanga-zanga domin nuna damuwa da tsarin da gwamnatin ƙasar ta amince da shi na tsuƙe bakin aljihu. Mutane kamar dubu 50 ne suka bazu akan titunan Dublin babban birnin ƙasar. A farkon wannan mako ne gwamnatin ta ƙasar Ireland ta gabatar da tsarin kasafin da ta na cike giɓi a tsawon shekaru huɗu wanda zai samar wa ƙasar da kuɗaɗe biliyan dubu 15. Sai dai a sakamakon wannan tsari gwamnatin za ta rage kuɗaɗen fansho da na albashi tare kuma da ƙara kuɗaɗen haraji.
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita: Halima Balaraba Abbas