Zanga zanga a kasar Girka
October 19, 2011'Yan 'sanda a birnin Athens na ƙasar Girka sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye wajan tarwatsa wasu matasan da suka rufe fuskokinsu da riguna masu huluna .A gangami da sama da mutane dubu 100 suka gudanar domin nuna rashin amince wa da matakin tsuke bakin aljihu da gwamnatin ta dauka ''wani ɗan ƙasar kenan ya na mai cewa sakamakon wannan shiri na gwamnatin ma'aikata da dama ne zasu rasa aiki, ya ce ga kuma wahalolin rayuwa.
A halin da ake ciki dai makarantu da bankuna da ofisoshin gwamnati da kuma al 'amuran sufuri sun tsaya cik a sakamakon yajin aiki na kwanaki biyu. Nan gaba ne dai majalisar dokoki ta ƙasar ta Girka za ta kaɗa ƙuri'a akan shirin tsuke bakin aljihu wanda ƙasar ta cimmawa tare da kungiyar Tarrayar Turai da kuma hukumomin lamuni na duniya;shirin ya tanadi rage kuɗaɗen albashin ma'aikata da rage kuɗaɗen fansho da kuma kara yawan haraji tare da rage yawan ma'aikatan gwamnati .
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar