Zanga zanga a kasar Pakistan
April 14, 2006Talla
Harkoki sun tsaya cik a birnin Karachi na kasar Pakistan yayinda duban jamaa suka fito zanga zanga tare da yajin aiki wanda shugabannin addini suka kira a yi,dangane da kunar bakin wake da ya kashe manyan shugannami yan sunni da wasu kuma 50 cikin wannan mako.
Harin na kunar bakin wake ya kashe dukkanin shugabannin wata kungiyar sunni Tehreek da wasu mutane 50,wajen bikin maulidi a kasar ta Pakistan.
Yanzu haka yan sanda da sojoji sun bazu koina birnin na Karachi mai mutane miliyan 15.
Gwamnati dai ta sha alwashin shiga kafar wando daya da duk wanda ya nemi kwasar ganima ko lalata dukiyoyin jamaa a lokacin zanga zangar.