Jagoran Falasdinawa ya yi wa wasu kasashe bazana
February 2, 2020Talla
Tun da farko masu zanga-zangar dauke da tutocin Falasdinu sun yi jerin gwano a Arewa maso Gabashin birnin Beirut suna sukar lamirin Amirka duk da irin matakin tsaron da mahukunta suka dauka don tsaron ofishin jakadancin na Amirka.
A ranar Asabar dai ne jagoran Falasdinawa Mahmoud Abbas ya yi barazanar yanke hulda da kasashen Isra'ila da Amirka yayin da yake jawabi a taron shugabannin kasashen Larabawa, bayan ministocin kasashen wajen kasashen na Larabawa sun zargi Amirka da yunkurin mayar da hannun agogo baya a samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.