Zanga-zanga a Masar kan Mursi
January 8, 2014Alkalin da ke sauraron shari'ar hambararren Shugaban kasar Masar Mohamed Mursi, ya dage sauraron karar zuwa ranar daya ga watan gobe na Febrairu, saboda yadda rashin yanayi ya hana kawo tsohon shugaban zuwa kotu.
Jami'ai sun ce saboda rashin kyan yanayin sararin samaniya, ya hana dauko Mursi daga inda ake tsare da shi a garin Alexandria, domin kawo shi Alkahira babban birnin kasar da jirgin sama mai saukan ungulu. Wannan ya zama karo na biyu da ake sauya lokacin shari'ar, na farko cikin watan Nuwamba.
A bayyanar da Mursi ya yi gaban kuliya cikin watan Nuwamban bara dai ya bayyana cewar bai amince da kotun da ba, kazalika ya ce har yanzu shi ne halartaccen shugaban Masar.
Magoya bayan hambararen shugaban Mursi sun gudanar da zanga-zanga a birnin na Alkahira, inda aka tsaurara matakan tsaro, kuma akwai wasu 'yan kungiyarsa ta Uwa Musulmai 14 da ake tuhuma tare da shi. Kasar ta Masar ta fada cikin rudani siyasa bayan sojoji sun kifar da gwamnatin Mohamed Mursi cikin watan Yuli na shekarar da ta gabata ta 2013.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu