1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga zanga a Masar na yin ƙamari

January 27, 2011

'Yan sanda na cigaba da yin artabu da masu zanga zanga a Masar.

Masu zanga zangar adawa da gwamnatin Hosni MubarakHoto: AP

A ƙasar Masar an shiga rana ta uku na jerin zanga zangar adawa da gwamnatin bayan da jama'a suka bujirewa dokar haramta zanga zangar inda suka ci-gaba da kiran kawo ƙarshen shekaru 30 na mulkin kama karya na shugaba Hosni Mubarak. 'Yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa da harsasan roba domin tarwatsa gangamin masu zanga zangar a birnin Alkahira. A cewar Jami'an tsaron na Masar sun tsare mutane kimanin 500. A ranar laraba ɗan sanda ɗaya da kuma wani daga cikin masu zanga zangar sun rasa rayukansu a lokacin tarzomar a Alkahira wanda ya kawo adadin mutanen da suka rasu a zanga zangar zuwa mutane shida. Wani mai magana da yawun tsohon shugaban hukumar makamashin nukiliya na Majalisar Ɗinkin Duniya Mohammed el-Baradei yace yana shirin zai dawo Masar domin shiga ayarin zanga zangar adawar da gwamnati. El-Baradei wanda ya karɓi lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel, shi ne babban wanda ke ƙalubalantar shugaba Hosni Mubarak wanda kuma ya sami goyon bayan masu ra'ayin kawo sauyi. A waje guda kuma sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton ta buƙaci kwantar da hankula inda ta yi kira ga mahukuntan na masar su yi amfani da wannan dama wajen aiwatar da sauyi a matakan siyasa da tattalin arziki da kuma jin daɗin rayuwar al'uma domin biyan muradun jama'ar Masar baki ɗaya. Ta na mai cewa Amirka a shiriye ta ke a ko da yaushe su yi yiki tare domin cimma wannan manufa.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala

Edita Usman Shehu Usman