1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zanga a Masar

June 8, 2012

Dubban jama'a sun tattaru a Dandalin Tahrir na birnin Alƙahira domin adawa nuna ga takara Ahmed Shafiq.

Protesters demonstrate after a court sentenced deposed president Hosni Mubarak to life in prison at Tahrir Square in Cairo June 2, 2012. Mubarak was sentenced to life in prison on Saturday for ordering the killing of protesters during the uprising that swept him from power last year. REUTERS/Mohammed Salem (EGYPT - Tags: POLITICS CIVIL UNREST CRIME LAW)
Hoto: Reuters

Dubban al'ummar Masar ne suka gudanar da boren bukatar haramta tsohon Firaministan Hosni Mubarak, Ahmed Shafiq daga takarar zaɓen shugaban ƙasa zagaye na biyu. Masu zanga-zangar kazalika sun yi Allah wadan hukuncin ɗaurin rai da rai da aka yanke wa tsohon shugaba Mubarak da jami'an tsaronsa, tsaka tsakin rahotannin dake nuni da ƙaurar da tsohon shugaban ƙasar dake fama da rashin lafiya, daga gidan waƙafi zuwa asibtin sojojin domin samun jinya. A ranar biyu ga watan Yuni ne dai aka yanke wa Mubarak da ministan harkokin cikin gidan Masar na da, Habib al-Adly, hukuncin ɗaurin rai da rai, sai dai kotun ta sallami kwamandojin rundunar 'yansandan Masar ɗin guda shida. A dandalin taro na Tahrir dake birnin Alƙahira, inda a bara aka yi gangamin kifar da gwamnatin Mubarak dai, sama da mutane 5,000 ne suka taru domin boren adawa da hukuncin kotun da kuma takarar tsohon Firamistan.

Ahmed Shafiq wanda ya samu nasarar zuwa zagaye na biyu a zaɓen shugaban ƙasar ta Masar, yayi alƙawarin ba da 'yancin walwala da faɗan albarkacin baki, idan ya zama shugaban ƙasa.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita: Yahouza Sadissou Madobi