Zanga zanga a Pakistan
January 9, 2011Dubban Jama'a sun gudanar da zanga zanga a Pakistan inda aka ƙiyasta cewa sama da mutane dubu 20 suka fito kan tituna, domin nuna ƙin amincewa da yin koskorima ga wasu dokokin shari'ar musulumci masamman ma akan hukumcin kisa. Zanga zangar wacce kungiyoyin musulmi masu tsatsauran ra'ayi suka tsara na kawo kuma goyon bayan ga wani ɗan sandar da ake tsare da shi.
Wanda a makon jiya ya bindige gwamna lardin Pundjab Salman Taseer wanda ake yi ma kallon mai neman kawo sauyi ga tsarin dokokin musulumuci. Tun can da farko Taseer din na kokarin gani an soke hukumci kisa da aka yankewa wata Kirista da aka tuhuma da laifin yin sabo akan Manzon Allah aminci Allah da tsira su tabata akansa, abinda ya janyo masa ƙaurin suna. A can ma cibiyar tattalin arziki na ƙasar wato Karashi, kusan mutane dubu 40 suka yi zanga zanga, kuma jama'ar sun gudanar da zanga zanga ce duk da ma yadda gwamnatin ƙasar ta bada sanarwa a farkon wannan mako cewa ba ta da niyar kawo canji ga dokokin ƙasar. Masu aiko da rahotannin sun ce wannan ita ce zanga zanga mafi girma da aka taba yi a ƙasar.
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu