1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Zanga-zangar magoya bayan Khan

Suleiman Babayo ZUD
November 26, 2024

Magoya bayan tsohon Firaminista Imran Khan na kasar Pakistan sun kutsa babban birnin kasar suna neman ganin an sake shi, tare da watsi da tuhume-tuhumen da ake yi masa da ake gani suna da dangantaka da siyasa.

Pakistan - Zanga-zanga a birnin Islamabad
Zanga-zanga a birnin Islamabad na kasar PakistanHoto: Irtisham Ahmed/picture alliance/AP

Kimanin jami'an tsaron Pakistan shida suka halaka yayin yunkurin tsayar da magoya bayan tsohon Firaminista Imran Khan suke kokarin shiga babban birnin kasar Islamabad suna neman ganin an sake shi daga gidan fursuna. Fiye da jami'an tsaro 100 suka jikata sakamakon artabu tsakanin masu zanga-zangar da kuma jami'an tsaro.

Karin Bayani: Pakistan: Ana fama da matsalar gurbacewar muhalli

Masu zanga-zangar suna neman ganin gwamnatin kasar ta sako tsohon Firaminista Imran Khan wanda yake garkame a gidan fursuna, kuma yana fuskantar tuhume-tuhume masu yawa. Tuni Firaminista Shehbaz Sharif na kasar ta Pakistan ya fitar da sanarwar inda ya yi tir da matakin masu zanga-zangar wadanda ya zarga da kin bin hanaoayi na lumana, inda suke neman tayar da hargitsi cikin kasar.