1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Zanga-zanga a Senegal ta kashe dalibi mai karatun likita

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 10, 2026

Hatsaniyar ta barke a jami'ar Cheikh Anta Diop ta birnin Dakar, inda jami'an tsaro suka kutsa cikin makarantar.

Harabar jami'ar Cheikh Anta Diop a birnin Dakar na Senegal
Harabar jami'ar Cheikh Anta Diop a birnin Dakar na SenegalHoto: Eddy Peters/Xinhua/imago images

Hukumomi a Senegal sun tabbatar da mutuwar wani dalibi mai suna Abdoulaye Ba, da ke karatun likita, sakamakon arangama da 'yan sanda yayin zanga-zangar nuna fushi da rashin biyan alawus din dalibai.

Hatsaniyar ta barke ranar Litinin, a jami'ar Cheikh Anta Diop ta Dakar babban birnin kasar, inda dubban dalibai suka tada bore, nan da nan jami'an tsaro suka kutsa cikin makarantar, tare da tarwatsa taron da hayaki mai sa hawaye, yayin da daliban ke jifansu da duwatsu, kamar yadda hotuna da faya-fayan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta suka nuna.

Karin bayani : Senegal ta ba wa hambararren shugaban Guinea-Bissau mafaka

Gwamnatin Senegal wadda ke fama da matsain tattalin arziki, ta mika sakon ta'aziyyarta ga iyalan mamacin, ta cikin sakon da mai magana da yawunta Marie-Rose Khady Fatou Faye ta fitar a wannan Talata.