Zanga-zanga kan dimukuradiyya ta yi ajalin mutane a Kenya
July 7, 2025
Masu rajin kare hakkin dan Adam na yin gangami kowace shekara a ranar 7 ga Yuli domin tunawa da ranar da a shekarar 1990 'yan adawa suka fara gwagwarmayar mayar da kasar zuwa tsarin jam'iyyu fiye da daya. Ana kiran wannan zanga-zanga da "Saba Saba" – wato "bakwai bakwai" a harshen Kiswahili – saboda kwanan wata na 7/7.
Hukumomi sun baza 'yan sanda a Nairobi tun bayan zanga-zangar matasa da ta faru a watanYuni 2024, wadda ta fara da adawa da karin haraji, amma daga baya ta rikide zuwa nuna kin jinin cin hanci,cin zalin da 'yan sanda ke wa jama'an gari da kuma yawaitar bacewar masu sukar gwamnati.
Wani ganau ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa 'yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye da ruwan zafi domin tarwatsa masu zanga-zanga a wata muhimmiya hanya a cikin birnin Nairobi, inda daruruwan masu zanga-zangar ke tafiya suna busa 'kusur' domin nuna cewa ba gudu, ba ja da baya.