Ekwado: Tarwatsa masu bore da zanga-zanga
October 9, 2019Talla
Arangama ta barke tsakanin jami'an tsaron Ekwado da masu bore da zanga-zangar nuna fushi kan karin kudin farashin man fetir, biyo bayan sun samu kutsawa a cikin harabar majalisar na wani dan lokaci.
Wannan lamarin na faruwa ne a daidai lokacin da dubban jama'a ke shirin fitowa gudanar da wata gagarumar zanga-zanga domin karba kiran kungiyoyin kwadago da suka yi fatali da hauhawar farashin man fetir.
Bore da zanga-zangar al'umma da ke ci gaba da dumi na kara ta'azzara harkokin yau da kullum da ma tabarbar da aikin hakar man fetur din kasar Ekwado.