1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Zanga-zanga na ci gaba da tsanani a Los Angeles na Amurka

June 9, 2025

Jami'an tsaro sun rika harbi da harsashin roba kan masu zanga-zanga a yayin da su kuma suka rika jifa da duwatsu.

Masu zanga-zangar na nuna adawa ne ga matakin shugaba Donald Trump na korar 'yan ci-rani.
Masu zanga-zangar na nuna adawa ne ga matakin shugaba Donald Trump na korar 'yan ci-rani.Hoto: Ethan Swope/AP Photo/picture alliance

Zanga-zanga na ci gaba da kara tsanani a birnin Los Angeles na Amurka a yayin da aka shiga wani sabon mataki na nuna adawa da aika jami'an tsaron kasa da shugaba Donald Trump ya yi don dakile zanga-zangar nuna kyama ga korar 'yan ci-rani. Dandazon mutane sun rika kunna wa motoci wuta tare da katse hanyoyi a birnin duk da kokarin hukumomi na taka musu birki.

Jami'an tsaro sun afka wa masu zanga-zanga a Amurka

Su kuwa jami'an tsaro sun rika fesa hayaki mai sa hawaye da kuma harbi da harsasan roba don tarwatsa dubban masu zanga-zangar.

'Yansanda sun haramta duk wata taruwar jama'a inda suka rika kama mutanen da suka ki watsewa bayan korar da dama a ranar Lahadi da dare. Wasu daga cikin mutanen da suka ki tafiya sun rika jifan motocin 'yansanda da duwatsu da ma kankare daga wurare da suka yi likimo.

'Yan sandan Amurka sun kama daliban jami'a masu goyon bayan Falasdinawa

Dubban mutanen na zanga-zangar nuna adawa ce da matakin shugaba Trump na korar 'yan ci-rani da suke birnin da kuma wasu sassan Amurka.