Neman sake bude kasuwanni a Burkina Faso
April 27, 2020Talla
Tun a ranar 20 ga watan Aprilu ne hukumomin kasar Burkina Faso suka bayyana matakin rufe manyan kasuwannin birnin Ouagadougou da Bobo-Dioulasso birni na biyu mafi girma a kasar a wani mataki na takaita yaduwar Corona, wacce ta yi sanadiyar mutuwar mutun 42 a kasar.
Dauke da allunan da ke nuna fushinsu kan matakin ci gaba da rufe kasuwannin, 'yan kasuwar na Burkina Faso sun ce shirye suke da su girmamam duk wasu matakan da likitoci suka gindaya na kariya muddin hukumomin kasar suka sake bude kasuwannin.