1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Jihar Rivers ta Najeriya na kara yin kamari

Muhammad Bello AH
December 20, 2023

Bayan yunkurin shugaban Najeriya na shiga tsakani domin magance rikicin siyasa Jihar Rivers, rikicin na kokarin kara fada a wasu jihohin a wani abin da ake ganin karon bata tsakanin APC da PDP.

 Tun bayan matakin sasantawada shugaban Najeriya da kuma wasu gaggan 'yan siyasar Rivers da kusoshin gwamnatin ta shugaban kasa, kan rikicin siyasar Rivers, da alamu matakin bai yi wa dattawan jihar da ma na daukacin yankin na Niger Delta dadi ba. Inda wasu ke kokarin zuwa kotu kan haka. Rigimar dai yanzu a jIhar ta Rivers ta dau salo na fada tsakanin kabilar Ijaw ta gwamna Fubara da kuma bangaren  gwamnan.

Bijerewar jama'ar yankin a kan sasantawar da shugaban Najeriya ya yi

Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP

Bisa dai matakin shiga tsakani da shugaban kasar ya yi kan rikicin siyasar ta Rivers, da matakin hakan ya kai ga cimma wasu yarjejeniyoyi takwas don a samu maslaha   tsakanin bangarori biyu masu rikici da juna, wato tsohon gwamna Nyesom Wike da kuma gwamnan jihar Siminalayi Fubara,da daman jama'ar jIhar ta  Rivers , musamman ma kabilar Ijaw a jhIar da ma yankin Niger Delta, na ganin ko kadan ba adalci a wannan sulhu da shugaban kasa ya yi, kuma ma suka ce ya yi wa dokar kasa da ta shari'a karan tsaye. Elder Edwin Clark, dattijo ne mai kima kwarai a yankin Niger Delta, kuma shi da 'yan kabilar Ijaw a yankin sun gudanar da taron tattaunawar rashin aminta da salon sulhu da shguban.

Rikicin na Jihar Rivesr na shirin zuwa gaban kotu a cewar dattawan yanki

Hoto: Temilade Adelaja/REUTERS

Tuni dai kungiyoyi sa kai da ma na majalisar matasan kabilar Ijaw suke ta Allah wadai da tsarin da ke cikin sulhun da aka yi, wanda suka ce an keta mutuncin mulkin dimokaradiyya. Madam AnnKio Briggs na daya daga dattawan yankin: Muna da gwamna amma wani mai juya gwamna na ganin shi ne gwamnan, to ba za mu yarda da hakan ba daukacin mu 'yan Jihar Rivers,kuma zaman sulhu da a ka cimma yarjejeniyoyi takwas ,mu jama'ar Rivers ba za mu yadda da haka ba,domin an taka dokar kundin tsarin mulkin Najeriya ,da 'yanci, kuma sakamkon rashin adalcin da ke cikin wannan sulhu, tuni mun fara shirya takardun mu don zuwa kotu don fassarar ka'idar da ke akwai, kan yadda shugaban kasa ya yi watsi da hukuncin kotu kan 'yan majalisu da ma shugabancin majalisa,inda ya yi gaban kan sa kan umartar wani abu daban.