Zanga-zanga ta barke a Nijar
July 30, 2023Rahotanni daga Yammai babban birnin Jamhuriyar Nijar sun yi nuni da cewa, masu zanga-zangar nuna goyon baya ga gwamnatin mulkin soji a kasar sun yi cikar kwari a gaban ofishin jakadancin Faransa bayan da gwamnatin Paris ta sanar da dakatar da bai wa Nijar din taimakon raya kasa.
Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa, masu boren sun yi yunkurin shiga cikin gini, yayin da wasu suke cire tambarin ofishin jakadancin tare da maye gurbinsa da tutocin Nijar da kuma Rasha.
An kuma ruwaito cewa, masu boren goyon bayan sojoji a Nijar din sun yi tada jijiyoyin wuya tare da ihun nuna goyon baya ga shugaba Vladmir Putin na Rasha.
Tuni dai Faransa ta yi Allah wadai da boren tare da mika bukata ta a gaggauta daukar matakin yi wa tufka hanci. A cikin sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Faransar ta fitar, ta ce ya zama wajibi hukumomin tsaron su tabbatar da tsaron jami'anta kamar yadda yarjejeniyar Vienna ta tanada.