SiyasaJamus
Zanga-zanga ta sake barkewa a kasar Sudan
October 30, 2021Talla
Shaidun gani da ido sun ce jama'a da dama ne suka fito kan tituna a Omdourman da Khartum, domin amsa kiran masu fafutikar ganin an sake mayar da mulki a hannun farar hula a Sudan. A ranar Litinin da tagabata ne jagoroan juyin mulkin Janar Abdel Fattah al-Burhane ya bayyana rushe daukacin hukumomin gwamnatin rikon kwarya da ke karkashin jagorancin fararen hula baya ga kama firaministan wucin gadi, lamarin da ya kara jefa kasar cikin rudanin siyasa.
Ko da yake an sallami hamabararren firaministan Abdallah Hamdok, amma ana ci gaba da tsare wasu da dama daga cikin mambobin gwamnatinsa, lamarin da kuma ya kara janyo wa gwamnatin mulkin soja mummnan suka daga kasashen duniya.