Zanga zangar ɗallibai da ƙungiyoyin ƙwadago a France
March 21, 2006Talla
A ƙasar france ƙungoyin ƙwadago da na yan makaranta, na ci gaba da zanga zanga, domin nuna adawa da sabuwar dokar ɗaukar ma´aikata, da gwamnatin Praminista Dominique de Villepin ta ɓullo da ita.
Wannan doka, ta tanadi baiwa shugabanin kampanoni damar ɗaukar sabin ma´aikata, a matsayin gwaji, har tsawan shekaru 2.
Su na kuma da yancin sallamar su, a ƙarshen wannan wa´adi ba tare da kace nace ba.
Gwamnati ta bayyana ɗaukar wannan doka, da zumar samar da ayyukan yi, ga ɗimbin matasa da ke fama da zaman kashe wando.
A nasu gefe ƙungiyoyin ƙwadago, da na yan makaranta, da ma yan adawa, sun ɗauki dokar a wani mataki, na taɓarbarra da, rayuwar matasa.
A ranar yau talata, jami´o´ i 67, daga jimmilar jam´o ´i 84 ,na ƙasar sun fuskanci zanga zanga.