1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar adawa a Aljeriya

January 23, 2011

Mutane 42 sun jikata a wani yunkurin gudanar da zanga-zanga da jam'iyyar adawa ta shirya a Aljeriya bisa hauhawar farashin kayan abinci.

Matasa masu arangama da 'yan sandaHoto: AP

Mutane aƙalla guda 42 suka jikata a ciki harda 'yan sanda bakwai a wani yunƙurin zanga-zanga da jam'iyyar adawa a ƙasar Aljeriya ta yi a birnin Algiers wanda ya ci tura. Masu aiko da rahotanin sun ce zanga-zangar wacce tun da farko hukumomkin ƙasar suka haramta daga bisani 'yan sanda sun tarwatsa jama'ar da suka yi dandazo a cibiyar jam'iyyar adawa ta RCD da nufin yin maci zuwa fadar gwamnati.

Ɗan zanga-zanga da ya samu rauniHoto: AP

Da ya ke magana ga manema labarai shugaban jam'iyyar adawar ta ta RCD, Said Sadi ya ce mutane da dama sun samu raunuka sannan kuma ya ce 'yan sanda sun kama kusan mutun biyar.

Tun a farkon wannan wata ne ƙasar ta Aljeriya ta yi fama da yamutsi na kusan kwanaki biyar a sanadin hauhawar farashin kayan abinci da ya hadassa tsananin tsadar rayuwa, wanda a cikinsa mutane biyar suka mutu yayin da wasu 800 suka jimu kafin daga bisanin gwamnatin ta karya farashin cimakar domin kwantar da hankulan jama'a.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita: Halima Balaraba Abbas