Zanga-Zangar adawa a Guinea
April 14, 2015A kasar Guinea an cigaba da zanga-zangar da jam'iyyun adawar kasar suka soma a kusan ko'ina a manyan biranen kasar domin nuna rashin amincewarsu da matakin gwamantin kasar na canza jadawalin zabukan da ta ke shirin gudanarwa a karshen wanann shekara.
Tun da sanyin safiyar talata ne dai daruruwan matasa magoya bayan jam'iyyun adawar kasar ta Guinea suka sake fantsama titunan babban birnin kasar wato Conakry, suna ta kona tayoyi abun da ya haddasa cunkuson ababan hawa a cikin birnin. Jami'an kwantar da tarzoma sun yi amfani da barkonon tsohuwa da kuma kulake wajen tarwatsa masu zanga zangar da su ka yi ta mayar da martani da harasahen mahaukacciya.
Sai dai wasu shaidun gani da ido sun ta tabbatar da cewa yan sanda sun cabke a dama daga cikin masu zanga zangar wadanda wasunsu a bisu ne har a cikin gidajansu. Mafi yawancin kasuwannin da ma makaramtun babban birnin kasar dai sun kasance a rufe a yau.
Barazanar da 'yan adawa suka yi
'Yan adawar dai sun sha alwashin yada wannan zanga-zanga tasu zuwa sauran manyan garuruwan kasar matsawar dai ba su samu biyan bukata ba. Abubacar Sylla shine kakakin kawanacan jamiyyun adawar kasar.
A wanann mako mun fara da birbin Konakri kuma a mako mai zuwa za mu yada zangazangar tamu zuwa sauran yankunan kasar kuma muna tabbatar maku da cewa babu kakkwautawa matsawar gwamnati ba ta share mana hawayemmu ba. Kuma a daina kallommu a matsayin wata adawa da ke da nufin dagula harakokin gwamnati .a a mu a bun da mu ke bukata shine a kiyaye doka kawai.
Yan adawar dai na wanann zanga zanga ne domin nuna rashin amincewarsu da matakin gwamnatin kasar na dage zaban kananan hukumomi har sai bayan an gudanar da na shugaban kasa da zai gudana a karshen wannan shekara ta 2015: Matakin da yan adawar su ka ce wani sale sali ne na neman tabka magudi a zaben shugaban kasar kamar dai yanda kakakin yan adawar ya yi karin bayani yana mai cewa.
Sun amince da jaddawalin zabe
Mu ba mu da wata tababa a game da jaddawalin da hukumar zabe mai zaman kanta ta tsara a game da zaben shugaban kasa.To amma muna tababa da aniyar gwamanti ta neman kin sake zaben shugabannin kananan hukumomi da doka ta tanadi zai gabaci na shugaban kasa. Alhali mun san gwamnati na son yin amfani da wadannan shugabannin kananan hukumomi wadanda a zahiri gwamnatin ce ta nada su ba zabar su aka yi ba. Ka ga kenan yan je-ka-na-yi-kan gwamnati ne wadanda a yau ta ke son yin amfani da su domin tabka magudi a zaben shugaban kasar mai zuwa.
Tuni gwamnatin kasar ta Guinea ta yi watsi da wanann zargi na 'yan adawa domin a cewarta tuni ta gayyaci masu sa ido na kasashen waje da su zo su halarci zaben domin tabbatar da ya gudana a cikin tsanaki