1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga zangar adawa da gwamnati a Faransa

Abdullahi Tanko Bala
December 15, 2018

Wasu kungiyoyin 'yan zanga zanga a Faransa da suka yi kunnen kashi wadanda kuma ke sanye da taguwa mai launin rawaya sun yi artabu da 'yan sanda a birnin Paris a wannan Asabar.

Frankreich Gelbwesten-Proteste in Paris
Hoto: Getty Images/AFP/Z. Abdelkafi

Ko da yake yawan masu zanga zangar dake adawa da gwamnatin ya ragu idan aka kwatanta da adadinsu a makonni biyar da suka gabata. Shugaba Emmanuel Macron wanda ke fuskantar kalubale mafi girma a mulkinsa, a ranar Litinin da ta gabata ya sanar da wasu jerin matakai na sassauci kan matsayin da ya dauka tun da fari, domin kwantar da wutar rikicin da ta karade Faransa a watan da ya gabata daga kauyuka zuwa birane.

Yana dai fatan soke karin haraji kan man fetur da kari kan mafi kankantar albashi ga kananan ma'aikata da kuma tsanannin sanyin hunturu da ake ake fuskanta a yanzu zasu sa al'amura su lafa fiye da makonnin baya.